Lahadi 12 Yuli 2026 - 16:07
Jagora Sheikh Zakzaky Ya Jaddada Muhimmancin Ilimi, Gwagwarmaya da Ikhlasi ga Ɗalibai a Mashhad

Hauza / Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), ya jaddada cewa ilimin da ɗalibai suke samu dole ne ya kasance a hidimar al'umma da kuma ci gaban Musulunci, yana mai bayyana cewa ilimin da ba a mayar da amfaninsa ga jama'a ba manufarsa ba ta cika ba.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran  Hauza, da yammacin ranar Asabar, 11 ga Yulin 2026, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya halarci bikin buɗe wani shirin horo na Mu'assasar Quds a birnin Mashhad, inda ya gana da ɗaliban Harkar Musulunci na Hauza da na jami'o'i daga biranen Qum, Tehran da Mashhad da ke karatu a Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Wannan shiri, wanda Mu'assasar Quds ke shirya wa a kowace shekara, ya ta'allaka ne kan nazarin littafin "Tarh-e Wilayah" na marigayi Ayatullah Muhammad-Taqi Misbah Yazdi (R), wanda ke bayyana ginshiƙan tunanin gwagwarmayar Imam Khumaini (QS) bisa bayanan Shahid Ayatullah Murtadha Mutahhari (R). A bana, an ware shirin ne ga ɗaliban na Harkar Musulunci, kuma zai gudana na tsawon kwanaki goma a birnin Mashhad.

A jawabinsa, Sheikh Zakzaky (H) ya sake miƙa ta'aziyyarsa kan shahadar Sayyid Ali Husaini Khamene'i (R), sannan ya ƙarfafa wa ɗalibai gwiwa da su himmatu wajen neman ilimi tare da mayar da amfaninsa ga al'umma. Ya ce kamar yadda mutum yake zuwa debo ruwa domin ya dawo gida a amfana da shi, haka ma ɗalibi ana sa ran zai samo ilimi ya dawo ya amfani al'ummarsa da abin da ya koya.

Jagoran ya kuma jaddada cewa duk ɗalibin da ya yi anfani da damar karatu da aka tanada masa, amma ya koma ƙasarsa ba tare da yin aiki domin kare addini da yi wa al'umma hidima ba, kamar ya yi wa Imam Mahdi (A.F) saddu ne. Ya yi kira ga ɗalibai da su haɗa ilimi da gwagwarmaya da kuma hidimar Musulunci.

A wani ɓangare na jawabinsa, Sheikh Zakzaky ya yi bayani kan muhimmancin yin aiki da ikhlasi saboda Allah. Ya ce duk aikin da aka yi saboda Allah, ladansa yana wajen Allah, amma wanda ya yi aiki saboda duniya kaɗai, rabonsa zai tsaya ne ga abin da ya samu a duniya.

Har ila yau, ya kawo wani labari mai cike da darussa domin bayyana muhimmancin biyayya ga umarnin Allah, aikata ayyukan alheri da kuma danne fushi. Ya bayyana cewa kame fushi (Kazmul-Ghaiz) yana daga cikin manyan siffofin bayin Allah na gari, musamman Imam Musa al-Kazim (A.S.), wanda aka san shi da wannan kyakkyawar ɗabi'a.

A ƙarshe, Sheikh Zakzaky (H) ya yi nuni da rayuwa da gwagwarmayar marigayi Shahid Sayyid Ali Husaini Khamene'i (Rahimahullah), yana mai bayyana cewa ikhlasi, haƙuri da jajircewarsa sun kasance abin koyi ga al'umma, kuma Allah Ya girmama shi da matsayi na shahada saboda sadaukarwarsa a tafarkinSa.

Jagora Sheikh Zakzaky Ya Jaddada Muhimmancin Ilimi, Gwagwarmaya da Ikhlasi ga Ɗalibai a Mashhad

Jagora Sheikh Zakzaky Ya Jaddada Muhimmancin Ilimi, Gwagwarmaya da Ikhlasi ga Ɗalibai a Mashhad

Jagora Sheikh Zakzaky Ya Jaddada Muhimmancin Ilimi, Gwagwarmaya da Ikhlasi ga Ɗalibai a Mashhad

Jagora Sheikh Zakzaky Ya Jaddada Muhimmancin Ilimi, Gwagwarmaya da Ikhlasi ga Ɗalibai a Mashhad

Jagora Sheikh Zakzaky Ya Jaddada Muhimmancin Ilimi, Gwagwarmaya da Ikhlasi ga Ɗalibai a Mashhad

Jagora Sheikh Zakzaky Ya Jaddada Muhimmancin Ilimi, Gwagwarmaya da Ikhlasi ga Ɗalibai a Mashhad

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha